Kamfanin Dillancin Labarun A.f.p daga birnin Moscow na kasar Rasha ya nakalto cewa; A JIYA litinin kasashen biyu su ka rattaba hannu akan yarjejeniyoyi makamashi da ya kunshi jigilar iskar gasa daga Siberia. Yarjejeniyar wacce pira ministocin kasashen Rasha Dmitry Medediv da kuma na Sin Li ke Tshayeng su ka halarci rattaba hannu akanta za ta fara aiki ne bayan tattaunawar da za a yi ta tsawon shekaru 10 a tsakanin kasashen biyu. Kuma daga shekara ta 1018 ne Rashan za ta fara turawa kasar Sin iskar gas din da a kowace shekara zai kai ma’aunin cubic mita triliyan 38. Kudin da Rashan za ta samu daga wannan yarjejeniyar zai kai dalar Amurka biliyan 400. Pira ministan kasar Rasha Mededev ya ce; Kasar Sin ita ce mai matsayi na farko a harkar kasuwancin da Rasha ta ke yi da kasashen waje. ABNA
14 Oktoba 2014 - 15:25
Lambar labari: 644317
Kasashen Rasha da Sin suna shirin kulla yarjejenyoyi 40 a tsakaninsu a cikin ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.